John 15

1“Nine itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomin. 2Yakan cire duk wani rashe a cikina da ba ya bada ‘ya’ya, mai bada ‘ya’ya kuwa ya kan gyara shi domin ya kara bada ‘ya’ya.

3Kun rigaya kun tsarkaka saboda maganar da na yi muku. 4Ku zauna ciki na, Ni kuma cikin ku. Kamar yadda reshe ba ya iya bada ‘ya’ya shi kadai sai ya zauna cikin itacen, haka kuma ba za ku iya ba, sai kun zauna ciki na.

5Ni ne itacen inabi, ku ne rassan. Wanda ya zauna ciki na, ni kuma cikin sa, yana bada ‘ya’ya dayawa, gama in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba. 6Wanda kuma bai zauna a ciki na ba, akan jefar da shi kamar reshe, ya bushe, kuma sukan tattara rassan su jefa a wuta, su kone. 7In kun zauna a ciki na, maganata kuma ta zauna a cikin ku, sai ku roki duk abinda kuke so, za a kuwa yi maku.

8Ta haka ake daukaka Ubana: cewa ku bada ‘ya’ya dayawa, kuma cewa ku almajiraina ne. 9Kamar yadda Ubana ya kaunace ni, haka Ni ma na kaunace ku; Ku zauna cikin kaunata.

10Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin kaunata kamar yadda Na kiyaye dokokin Ubana, na kuma zauna cikin kaunarsa. 11Ina gaya maku wadannan al’amura domin farincikina ya kasance a cikin ku, kuma domin farincikinku ya zama cikakke.

12“Wannan shine umarnina, cewa ku kaunaci juna kamar yadda na kaunace ku. 13Babu wanda ke da kaunar da tafi haka, wato ya bada ransa domin abokansa.

14Ku abokaina ne idan kuna yin abubuwan da na umarce ku. 15Nan gaba ba zan kara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abinda Ubangijinsa ke yi ba. Na kira ku abokaina, domin na sanar da ku duk abinda na ji daga wurin Ubana.

16Ba ku kuka zabe ni ba, amma Ni ne na zabe ku, na aike ku don ku je ku bada ‘ya’ya, ‘ya’yanku kuma su tabbata. Wannan ya zama domin duk abinda kuka roki Uba a cikin sunana, zai baku. 17Na baku wannan umarni: domin ku kaunaci juna.

18In duniya ta ki ku, ku sani cewa ta kini kafin ta ki ku. 19Da ku na duniya ne, da duniya ta kaunace ku kamar nata. Amma saboda ku ba na duniya bane, na kuma zabe ku daga duniya, don haka duniya take kin ku.

20Ku tuna da maganar da na yi muku, ‘Bawa ba ya fi Ubangijinsa girma ba.’ Idan sun tsananta mani, ku ma za su tsananta maku; Idan sun kiyaye maganata, za su kuma kiyaye maganarku. 21Za su yi maku duk wadannan abubuwa saboda sunana, don basu san wanda ya aiko ni ba. 22Da ban zo na yi masu magana ba, da basu da zunubi, amma yanzu, basu da wata hujja don zunubinsu.

23Duk wanda ya ki ni ya ki Ubana. 24Da ban yi ayyukan da babu wanda ya taba yinsu a cikin su ba, da basu da zunubi, amma yanzu sun gani, sun kuma ki ni da Ubana duka. 25An yi wannan kuwa domin a cika maganar da ke rubuce a cikin shari’arsu, ‘Sun ki ni ba dalili.’

26Sa’adda Mai Ta’aziya- wanda zan aiko maku daga wurin Uban, wato, Ruhun gaskiya, wanda ke fita daga wurin Uban-ya zo, zai bada shaida a kai na. Ku ma kuna bada shaida saboda kuna tare da ni tun daga farko.

27

Copyright information for HauULB